MDD-Fyade

Kasashe na son Majalisar Dinkin Duniya ta tsananta hukunci kan fyade

Majalisar Dinkin Duniya ta koka da yadda cin zarafin mata ta hanyar fyade ke ci gaba da tsananta a kasashen da ke fuskantar yake-yake.
Majalisar Dinkin Duniya ta koka da yadda cin zarafin mata ta hanyar fyade ke ci gaba da tsananta a kasashen da ke fuskantar yake-yake. CHARLY TRIBALLEAU AFP/File

Kasashen Duniya sun bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta kara yawan hukuncin da ake yiwa mutanen da ke amfani da tashe tashen hankula ko kuma yaki suna yiwa mata fyade.

Talla

Wannan ya biyo bayan rahotan binciken da aka yi wanda ya nuna karuwar cin zarafin matan da ake samu a kasashen da ake fama da tashin hankali musamman kasashen Habasha da Libya da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da kuma yankin Darfur na Sudan.

Denis Mukwege, likitan da ya samu kyautar Nobel saboda kular da ya ke bai wa matan da akaci zarafin su, ya ce cin zarafin mata ya zama ruwan dare, kuma rashin daukar mataki mai karfi akan su zai cigaba da karfafa masu aikata laifin.

Jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan yaki da cin zarafin mata Pramilla Parten ta ce a cikin wannan shekara kawai an samu mutane 52 da kungiyoyin da ke aikata irin wannan laifi, kuma sama da kashi 70 daga cikin su sun yi kaurin suna wajen aikata irin wannan laifin ganin yadda sunayen su su ke ta bayyana cikin kundin da ake aje masu laifin na tsakanin shekaru 3 zuwa 5.

Yayin da wasu wakilan kwamitin sulhu suka yi Allah wadai da matakin amfani da yaki wajen cin zarafin matan, kadan daga cikin su ne suka goyi bayan daukar matakai masu tsauri akan masu aikata laifin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.