Amurka-Minneapolis

'Yar sandar Amurka na fuskantar tuhuma kan kashe bakar fata a Minneapolis

Arangamar jami'an tsaro da masu zanga-zanga a birnin Minneapolis na jihar Minnesota a Amurka.
Arangamar jami'an tsaro da masu zanga-zanga a birnin Minneapolis na jihar Minnesota a Amurka. AFP - KEREM YUCEL

Masu Gabatar da kara a Amurka na tuhumar  'yar sandar da ta harbe wani matashi bakar fata Daunte Wright har lahira da laifin kisan kai, dai dai lokacin da ake ci gaba da fuskantar kakkarfar zanga-zanga a sassan birnin na Mninneapolis don adawa da yadda jami'an tsaro ke kashe bakaken fata ba tare da kaukautawa ba.

Talla

Tuni jami’ar ta aje kakin ta bayan aukuwar lamarin, kuma yanzu haka tana fuskantar hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari idan an tabbatar da laifi akan ta.

Lauyan iyalan Wright da aka kashe, sun yaba da matakin shari’ar da aka dauka amma kuma sun ce babu wani hukuncin da zai dawo musu da dan uwan su.

Zuwa yanzu an shiga kwana na 3 da fara zanga-zangar a sassan birnin yayinda aka kame mutane fiye da 60 bayan arangamarsu da jami'an tsaro.

Al'ummar birnin na Minneapolis sun matukar harzuka da kisan na baya-bayan nan musamman la'akari da yadda ya zo a dai dai lokacin da ake shari'ar kisan George Floyd da 'yan sanda suka yi da gangan a bara duk dai a birnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.