Covid-19-Rigakafi

Mawadata sun yi wa matalauta nisa a rigakafin Korona

Nau'in allurar rigakafin coronavirus
Nau'in allurar rigakafin coronavirus © iStock /kovop58

A daidai lokacin da ake kokarin wadatar da duniya da allurar rigakafin hana kamuwa da cutar COVID 19, yanzu haka ana ci gaba da samun gibi tsakanin al’ummomin da ke rayuwa a kasashe matalauta da kuma masu karfin tattalin arziki da ake yi wa allurar.

Talla

Yanzu haka kasashe mawadata na ci gaba da yi wa al’ummominsu allurar kariya daga wannan annoba, yayin da a sauran kasashen masu karafin karfi ake dakon samun wannan allura domin yi wa jama’a.

Wannan na daga cikin dalilan da suka sa shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO Ngozi Okonjo-Iweala ta kaddamar da wani yunkuri don samar da wannan allura a wadace.

A ranar Larabar da ta gabata, Okonjo-Iweala ta jagoranci taron da ya hada wakilan kamfanoni akalla 50 da suka hada da masu sarrafa magunguna, wakilan gwamnati da kuma sauran hukumomin kasa da kasa inda suka tattauna kan wannan batu.

Babbar manufar taron ita ce, gano bakin zare dangane da matsalolin da ke haddasa tseko har ma aka gaza wadata duniya da allurar rigakafin.

Daga cikin allurai milyan 885 da aka yi kawo yanzu a sassan duniya, kashi 48% an yi su ne a cikin kasashe mawadata da duka-duka yawan al’ummominsu bai wuce kashi 16% ba a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.