Cuba

Amurka ta yi kokarin kashe wasu daga cikin jagororin kasar Cuba

Raul Castro Shugaban kasar Cuba
Raul Castro Shugaban kasar Cuba AFP - ARIEL LEY ROYERO

A wasu bayyanan sirri da Amurka ta wallafa  na dada nuni cewa hukumar leken asirin kasar wato CIA  a shekara ta 1960 ,hukumar ta shawo kan matukin jirgi dake dauke da Raul Castro memba a jam’iyya mai mulki a lokacin zuwa gida daga birnin Prague. Matukin jirgin zai  hallaka shi a kan kudi dalla dubu 10.

Talla

Matukin jirgin na lokacin mai suna  Jose Raul  Martinez dake aiki karkashin hukumar leken asirin Amurka ta CIA ya bukaci hukumar ta dau nauyin karatun  ya’an sa biyu bayan mutuwar sa a wannan hatsari.

 To sai dai yan lokuta da cirawa, babban ofishin hukumar leken asirin Amurka ya umurci a soke batun, duk da cewa matukin bai samu  wannan umurni bayan  cirawar sa.Sai dai ya kasa janyo hatsarin jirgin kamar yada aka bukaci ya yi a baya.

Marigayi Tsohon Shugaban kasar Fidel  Castro ya tsallaka rijia da baya a  yukunrin hallaka shi daga Amurka sau 638.

Tsohon Shugaban kasar Fidel Castro da Shugaba mai ci Raul Castro
Tsohon Shugaban kasar Fidel Castro da Shugaba mai ci Raul Castro REUTERS/Desmond Boylan

Wadannan bayyanai na zuwa ne a wani lokaci da Shugaban kasar mai shekaru 89 ke shirin saki ragamar mulki ga matasa sabin jinni,wanda haka ke dada nuni cewa ana shirin shiga wani sabon babe dangane da siyasar Amurka da Cuba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.