Amurka - China

Amurka da China sun cimma matsayar aiki tare wajen yakar sauyin yanayi

Manzon Amurka na musamman kan sauyin yanayi John Kerry, da kuma ministan Harkokin wajen Koriya da Kudu Chung Eui-yong, ranar 17 ga watan Afrelun 2021.
Manzon Amurka na musamman kan sauyin yanayi John Kerry, da kuma ministan Harkokin wajen Koriya da Kudu Chung Eui-yong, ranar 17 ga watan Afrelun 2021. AP

Amurka da China sun "kuduri aniyar hadin gwiwa" kan batun yakar sauyin yanayi, kamar yadda bangarorin biyu suka bayyana jiya Asabar.

Talla

Sanarwar hadin gwiwar na zuwa ne bayan ziyarar da wakilin Amurka kan yanayi John Kerry ya yi zuwa Shanghai, jami'i na farko daga gwamnatin Biden da ya ziyarci China, yana mai nuna fatan bangarorin biyu za su iya yin aiki tare a kan kalubalen dake fuskantar duniya duk da sabani da suke samu a wasu bangarorin.

Sanarwar daga Kerry da wakilin musamman na China kan sauyin yanayi Xie Zhenhua ta ce "Amurka da China sun himmatu wajen yin hadin gwiwa da juna da kuma sauran kasashe don magance matsalar sauyin yanayi, wanda dole ne a magance shi cikin tsananin gaggawa."

Sanarwar ta lissafa hanyoyi da yawa na hadin gwiwar sauyin yanayi tsakanin Amurka da China, manyan kasashe biyu na duniya wadanda suka dauki alhakin samar da kusan rabin hayaki mai gurbata muhalli dake haifar da sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI