Amurka

Matar da tafi kowa tsufa a Amurka ta rasu tana da shekaru 116

Wasu daga cikin wurrae da ake adana gajiyayu
Wasu daga cikin wurrae da ake adana gajiyayu REUTERS/Mohamed Abd El Ghany

Matar da tafi kowa tsufa a Amurka Hester Ford ta rasu tanada shekaru 116 a lokacin da iyalan ta ke kewaye da ita.

Talla

Rahotanni sun ce Ford wadda aka haifa tsawon lokaci kafin gudanar da yakin duniya a daidai shekarar da aka kirkiro kankarar ‘ice cream’ da kuma shekarar fara aiki a mashigin ruwan Panama ta rasu ne a gidan ta dake Jihar North Carolina.

Bayanai sun ce Ford ta bar magada 288 da suka hada da yaya 12 da jikoki 48 da tattaba kunne 108 da yayan tattaba kunne 120.

Les personnes placées en maison de retraite peuvent recevoir de la visite.
Les personnes placées en maison de retraite peuvent recevoir de la visite. Getty Images/PeopleImages

Sanarwar da iyalan ta suka gabatar tace duk da rasuwar ta ayyukan da tayi lokacin rayuwar ta zasu cigaba da zama abin tunawa ga iyalan ta da sauran jama’a mussaman wadanda suka amfana da rawar da ta taka wajen ganin an inganta rayuwar jama’a.

Rahotanni sun ce babu wanda ya san ranar da aka haife ta, amma gwajin da akayi ya nuna cewar itace BaAmurkiya mafi tsufa.

Ford ta tashi ne a yankin karkarar dake South Carolina tana aiki a gonar auduga kamar yadda gidajen talabijin din WBTV dake alaka da CBS a Charlotte ya sanar, yayin da daga bisani tayi aiki na shekaru da dama a matsayi mai reno.

Mijin ta da suka kwashe shekaru 45 tare ya rasu a shekarar 1963 kuma tun daga lokacin bata sake aure ba.

Hukumar kididdigar Amurka tace a shekarar 2019 an gano cewar Ford ce mafi tsufa a Amurka bayan mutuwar Alelia Murphy mai shekaru 114.

A lokacin rayuwar ta da aka tambaye ta dalilin dadewar ta a duniya, sai tace tana fara karya kumallo da cin ayaba kowacce rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.