Coronavirus-Rigakafi

Alfanun rigakafin Korona sun fi rashinsu yawa-Farfesa Sabitu

Wani matashi kenan da ya karbi rigakafin coronavirus a Sudan
Wani matashi kenan da ya karbi rigakafin coronavirus a Sudan © AFP - Ebrahim Hamid

Mutane da dama a sassan duniya na ci gaba da dari-darin karbar allurar rigakafin Covid-19 saboda fargabar gamuwa da matsalar daskarewar jini da ka iya haddasa mutuwa kamar yadda aka gani a wasu kasashe.

Talla

A baya-bayan nan, kasar Denmark ta sanar da dakatar da amfani da allurar Astrazaneca baki daya saboda illolin da ta ce tana haddasawa da suka hada da daskarewar jini.

Kafin Denmark ta yanke wannan shawara, an samu kasashe da dama a Turai da suka dakatar da amfani da Astrazaneca kafin daga bisani su janye matakin dakatarwar.

Sai dai masana cutuka masu yaduwa irinsu Farfesa Kabir Sabitu na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a Najeriya sun ce, alfanun allurar rigakafin annobar sun fi rashin alfanunsu yawa, musamman idan aka yi la'akari cewa, mutane kalilan ne daga cikin miliyoyi ke kokawa ko kuma rasa rayukansu a dalilin allurar.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da RFI Hausa ta yi da Farfesa Kabir Sabitu kan wannan batu

 

Hira kan alfanun rigakafin Korona tare da Farfesa Kabir sabitu

 

Farfesan ya bayyana cewa, akasarin magunguna na da wasu illoli na daban, amma dai suna aikin warkar da cutuka.

Abubuwan rigakafin nan da aka samo su, watakila suna da kananan illoli, amma hakan bai nuna cewa, ba sa aiki ba. inji Farfesa Sabitu

Kasashen duniya sun kara kaimi wajen yi wa al'ummominsu allurar rigakafin cutar wadda kawo yanzu aka tabbatar cewa, ta lakume rayuka fiye da miliiyan uku baya ga mutane sama da miliyan 140 da suka harbu da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.