Cuba

Diaz-Canel ya maye gurbin Raul Castro a matsayin Shugaban Cuba mai cikakken iko

Miguel Diaz-Canel, Sabon Shugaban kasar Cuba
Miguel Diaz-Canel, Sabon Shugaban kasar Cuba REUTERS/Alejandro Ernesto/Pool/File Photo

Miguel Diaz-Canel ya maye gurbin Raul Castro a matsayin shugaban kasar Cuba mai cikakken iko, kana kuma shugaban Jam’iyar kwaminisanci, abinda ya kawo karshen mulkin shekaru 60 na iyalan Castro.

Talla

Diaz-Canel ya zama shugaban kasar Cuba tun daga shekarar 2018 amma bashi da ikon gudanar da wasu ayyuka wadanda suka rataya a wuyan Castro har zuwa yau litinin da ya aje aikin sa yana da shekaru 89 a duniya.

Raul Castro tsohon Shugaban kasar Cuba
Raul Castro tsohon Shugaban kasar Cuba Ariel LEY ROYERO ACN/AFP

Sabon shugaban ya zama farar hula na farko da ya jagoranci Cuba kuma mutuum na farko da bashi da alaka da iyalan gidan Castro wadanda suke jagorancin Cuba daga shekarar 1959 zuwa 2018 tsakanin Fidel da Castro. Fidel ya shugabanci Cuba daga 1959 zuwa 2006, yayin da kanin sa Raul ya karbi iko daga shekarar 2006 zuwa 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.