Coronavirus-Duniya

Korona ta lakume rayuka fiye da miliyan uku

Coronavirus ta lakume rayukan mutane sama da miliyan uku kawo yanzu
Coronavirus ta lakume rayukan mutane sama da miliyan uku kawo yanzu REUTERS - STRINGER

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce adadin mutanen da cutar Korona ta kashe ya zarce miliyan uku, yayin da cutar ke ci gaba da yaduwa duk da allurar rigakafin da ake yi wa jama’a a wasu kasashen duniya.

Talla

Alkaluman Hukumar Lafiyar sun ce, a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, ana samun akalla mutane dubu 12 da ke mutuwa kowacce rana, abin da ya kara yawan mutanen da annobar ke kashewa, inda yanzu suka kai miliyan 3 da dubu 11,975 daga cikin mutane sama da miliyan 140 da suka harbu.

Wadannan alkaluma na mutane miliyan 3 da suka mutu sun zarce yawan mutanen da ke kasashen Jamaica ko Armenia ko kuma yawan mutanen da suka mutu sakamakon yakin da aka gwabza tsakanin Iran da Iraqi tsakanin shekarar 1980 zuwa 1988.

Birnin Delhi da ke India da aka killace mutane a gidajensu a karshen wannan mako, ya nuna cewar an samu sabbin mutanen da suka harbu da cutar da yawansu ya kai dubu 234,000 a rana guda, yayin da 1,341 suka mutu.

Kasar India ce yanzu ta biyu wajen yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar bayan Amurka, yayin da Brazil ta koma matsayi na uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.