China

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta zargi China da azabtar da 'Yan kabilar Uighur

Wasu daga cikin masu zanga-zanga yan kabilar Uighur
Wasu daga cikin masu zanga-zanga yan kabilar Uighur REUTERS - TYRONE SIU

Kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch ta zargi China da hannu dumu dumu wajen aikata laifuffukan cin zarafin Bil Adama akan Yan kabilar Uighur Musulmi.

Talla

Rahotan da kungiyar ta gabatar na hadin gwuiwa tare da Cibiyar koyar da aikin lauya da sasanta rikice rikice dake Amurka ya zargi hukumomin China da tsare Yan kabilar Uighur sama da miliyan guda a Yankin Xijiang, yayin da ta tilastawa miliyoyi zama cikin mummunar yanayin da ake sanya ido akan su koda yaushe.

Rahotan binciken bangarorin biyu yace gwamnatin China ta aikata laifin cin zarafin Bil Adama kuma tana cigaba da aikata haka akan Yan Kabilar Turkic Musulmi bayan na Uighur.

Musulmai yan kabilar Uighur
Musulmai yan kabilar Uighur REUTERS - MURAD SEZER

Rahotan yace China tana daukar wannan mataki ne domin share al’adun mutanen da kuma addinin su, kuma hakan ya sabawa dokar duniya da aka amince da ita a Rome a shekarar 1998.

Bangarorin biyu sun zargi China da cigaba da tsarewa da azabtarwa da kuma kashe yan kabilar Uighur da kuma azabtar da su da gangan, kana da lalata da su

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.