Chadi-Faransa

Faransa ta bayyana Idriss Deby a matsayin jarumi

Marigayi shugaban Chadi Idriss Deby Itno tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron
Marigayi shugaban Chadi Idriss Deby Itno tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron © AFP - Ludovic Marin

Faransa ta jinjina wa marigayi shugaban Chad Idriss Deby Itno, wanda ta bayyana a matsayin jarumi kuma gwarzon soja, yayin da ta bukaci kwantar da hankula a kasar bayan mutuwarsa.

Talla

Wata sanarwa da ofishin shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya fitar ta ce,  Chadi ta yi rashin gwarzon soja kuma  jagoran da ya yi aiki tukuru wajen tabbatar da tsaro a kasarsa da kuma samar da zaman lafiya a yankin yammacin Afrika a tsawon mulkinsa na shekaru 30.

Sanarwar ta kuma jaddada muhimmancin zaman lafiya a Chadi ganin cewa, tana fuskantar barazanar hari daga ‘yan tawayen da ke kokarin dannawa cikin babban birnin N’Djamena.

Al’ummar Chadi na ci gaba da aikewa da  sakwannin ta’aziyarsu bisa rasuwar  shugabansu wanda ya ja numfashinsa na karshe a fagen  fafatawa da ‘yan tawaye kamar yadda sanarwar sojin kasar ta ce.

Farfesa Doughlas Yates da ke sashen nazari kan nahiyar Afrika a Kwalejin Amurka da ke birnin  Paris ya bayyana cewa, abin alfahari ne yadda shugaba Deby ya gamu da ajalinsa a fagen daga, ba kamar yadda wasu takwarorinsa ke mutuwa a kan gado a dalilin cutar Covid-19 ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.