Lokaci ya na kurewa Duniya a yaki da dumamar yanayi- MDD

Antonio Guterres ya bukaci duniya ta dauki matakai masu karfi da za su taimaka wajen shawo kan matsalar dumamar yanayi.
Antonio Guterres ya bukaci duniya ta dauki matakai masu karfi da za su taimaka wajen shawo kan matsalar dumamar yanayi. BJ KIRSCHHOFFER POLAR BEARS INTERNATIONAL/AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta ce lokaci na kurewa kasashen duniya wajen daukar matakan da suka dace da nufin kare jama’a daga illar sauyi ko dumamar yanayi.

Talla

Wannan gargadi na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban Amurka Joe Biden ke shirin kaddamar da taron yadda za a magance matsalar wanda zai gudana a ranakun alhamis da juma’a.

Shugabannin kasashen duniya 40 aka gayyata domin halartar taron wanda zai gudana ta hanyar bidiyo wanda shi ne na farko da Amurka ke jagoranci tun bayan dawowar ta cikin yarjejeniyar yanayi ta Paris.

Sakatare Janar na Majalisar Antonio Guterres ya bukaci shugabannin kasashen duniya su dauki matakai masu karfi da za su taimaka wajen shawo kan matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.