Amurka-Floyd

Kotu ta samu makashin Floyd da laifin kisa

Derek Chauvin na fuskantar hukuncin daurin shekaru 40 bayan kisan George Floyd
Derek Chauvin na fuskantar hukuncin daurin shekaru 40 bayan kisan George Floyd Handout Hennepin County Jail/AFP/Archivos

Kotun Amurka ta samu Derek Chauvin da laifin kashe bakar fatar nan George Floyd a shari’ar da aka yi masa sakamakon makure shi na dogon lokaci, hukuncin da ya gamu da farin ciki a sassan kasar.

Talla

Masu taimaka wa alkali yanke hukunci sun kwashe sa’o'i 11 suna tafka mahawara a tsakaninsu kafin cimma matsayar cewar, Chauvin ya aikata laifuka guda 3 da aka tuhume shi akai da suka hada da kisan kai ba tare da niyya ba da kuma makure George Floyd har sai da ya daina numfashi.

Wannan matsayi ya haifar da murna da kuma sowa daga mutanen da suka taru a harabar kotun da kuma wasu a sassan Amurka, yayin da wasu suka zubda hawaye saboda farin ciki kan yadda shari’ar ta kaya, musamman lokacin da alkali Peter Cahill ke karanat ta, kafin daga bisani 'yan sanda suka maka wa Chauvin ankwa suka fitar da shi daga kotun.

Ana sa ran kotun ta bayyana hukuncin daurin akalla shekaru 40 a gidan yari kan wanda aka asamu da laifin.

Yayin tsokaci kan hukuncin, fitaccen mai fafutukar kare yancin bakar fata a Amurka, Al Sharpton ya ce wannan ne karo na farko da aka samu wani dan sanda farar fata da laifin kashe bakar fata a tarihin kasar, yayin da dan uwan Floyd, Rodney ya ce bakaken fata sun dade suna fuskantar rashin adalci a Amurka.

Shugaban kasa Joe Biden ya kira iyalan Floyd ta waya inda ya bayyana farin cikinsa da hukuncin, wanda ya ce zai bude kofar tabbatar da adalci a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.