Canjin Yanayi

Biden na jagorantar taron kasashen duniya kan magance gurɓatar muhalli

Shugaban Amurka Joe Biden lokacin taron yanayi ta hoton bidiyo a fadar white house ranar 22 ga watan Afrelu 2021.
Shugaban Amurka Joe Biden lokacin taron yanayi ta hoton bidiyo a fadar white house ranar 22 ga watan Afrelu 2021. AP - Evan Vucci

Shugaban Amurka Joe Biden ya bude taron muhalli da ake saran shugabannin kasashe duniya 40 su gabatar da jawabi domin jaddada matsayin sun a yaki da gurbata muhalli.

Talla

Taron na kwanaki biyu da ake gudanar da shi ta kafar bidiyo, zai baiwa Amurka damar jaddada aniyar ta na yaki da gurbata muhalli sakamakon sauyin gwamnatin da aka samu a kasar, yayin da suma shugabannin duniya zasu bayyana shirin da suke da shi.

"A jawabin da ya gabatar na bude taron, shugaban Amurka Joe Biden yace babu wata kasa guda da zata iya shawo kan wannan matsala. Babu wata kasa da zata iya shawo kan wannan matsala ita kadai, kuma ina fata dukkan ku kun san haka. Dukkan mu, dukkan mu, musamman mu da muke wakilatar kasashen da suka fi habakar tattalin arziki, ya zama dole mu kara kaimi, wajen zuba jari a tsakanin jama’a a bangaren samar da makamashin da baya gurbata muhalli. Domin samun nasara."

 

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci daukan kwararan matakai a aikace domin ceto muhallin da ake da shi.

Muna yanayi mara kyau. Ya zaam dole mu fahimci cewar mataki na gaba da zamu dauka mai kyau ne. Ya dace shugabanni daga kowanne bangare su dauki mataki. Na farko yana da kyau mu samu hadin kai domin cimma buri nan da tsakiyar wannan karnin. Kowacce kasa, kowanne sashe, kowanne kamfani da kowacce masana’anta. Na biyu daukar wannan matakin cigaba, kowacce kasa daga cikin manyan kasashen da suka fi gurbata muhalli zasu gabatar da tallafin shirin yaki da gurbata muhalli na shekaru 10 masu zuwa kamar yadda aka shirya a shirin shekarar 2050. Na uku shine aiwatar da wadannan manufofi a aikace.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci daukan kwararan matakai a kan muhalli

Cikin shugabanin da suka gabatar da jawabi harda shugaban China Xi Jinping da Vladimir Putin na Rasha da Narendra Modi na India.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.