Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba hannunta a zaben shugaban kasar Syria mai zuwa

CHINA-RIGHTS/UN
CHINA-RIGHTS/UN REUTERS - POOL

Majalisar Dinkin Duniya ta ce babu ruwanta da zaben shugaban kasa da Syria ke Shirin gudanarwa nan gaba kadan.

Talla

Sanarwar na zuwa ne bayan da Majalisar Dokokin Syria ta sanar jiya Laraba cewa Shugaba Bashar al-Assad zai tsaya takaran shugabancin kasar a zaben da za su yi  ranar 26 ga watan gobe,

Zaben zai kasance shine na biyu a shekaru 10 da kasar ke cikin yaki.

Mai Magana da yawun babban sakatare-Janar na MDD Antonio Gutteres, wato Stephane Dujariric ya ce MDD na bukatar a warware rikicin Syria ta siyasa ba yaki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.