Malaria

An samu nasarar gwajin wani sabon maganin zazzabin malaria

Sauro nau'in Anopheles gambiae da ke haddasa zazzabin malaria.
Sauro nau'in Anopheles gambiae da ke haddasa zazzabin malaria. AFP/File

Wasu Masana a Birtaniya sun bayyana samun gagarumar nasara a kan gwajin da suka yi wa wani sabon maganin cutar zazzabin cizon sauro, ko kuma malaria wanda suka ce ingancinsa ya kai kashi 77 a gwajin da aka yi wa yara kanana.

Talla

Maganin rigakafin da aka yi wa lakabi Matrix-X da Cibiyar Jenner da ke Jami’ar Oxford ta samar an gwada shi ne a kasar Burkina Faso kuma ya yi tasirin da ya kai kashi 77 a kan yara 450 da aka yi wa allurar a shekarar 2019, kuma an gano ba shi da wata illa.

Masanan sun ce wannan shine maganin cutar malaria na farko da ingancin sa ya zarce mizanin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta gindaya wa masu binciken kimiyya, wanda ya zarce kashi 75 nan da shekarar 2030.

Masanan sun ce za’a sake yin wani gwajin da zai shafi yara kanana 4,800 a kasashen Afirka guda 4 a wani hadin gwiwa da Cibiyar kula da lafiyar Serum da ke India, da kuma kamfanin hada magungunan Novavax da ke Amurka.

Farfesa Adrian Hill, shugaban Cibiyar Jenner da ta samar da maganin rigakafin cutar korona da kamfanin AstraZeneca ke rarrabawa a kasashen duniya ya bayyana sakamakon gwajin a matsayin babbar al'amari dangane da yakin da ake da cutar malaria.

Hill ya ce suna bukatar kara kaimi domin kauce wa samun matsala, ganin irin nasarar da aka samu.

Yayin da ake shirin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro wanda ke kashe mutane akalla 400,000 kowace shekara  a ranar Lahadi mai zuwa, Hukumar Lafiya ta duniya ta ce kawar da cutar baki daya na da matukar muhimmanci ga kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.