India-Coronavirus

Kasashen duniya na rige-rigen ceto India daga mutuwa

India na matukar fama da karancin iskar Oxygen da ke taimaka wa masu Korona numfashi, abin da ya sa ta nemi taimakon kasashen duniya.
India na matukar fama da karancin iskar Oxygen da ke taimaka wa masu Korona numfashi, abin da ya sa ta nemi taimakon kasashen duniya. Sajjad HUSSAIN AFP

Kasashen duniya sun sanar da shirinsu na tallafa wa India wadda annobar Covid-19 ke ci gaba da lakume mata rayukan al’umma babu kakkautawa, inda Kungiyar Tarayyar Turai ta ce, tana kan tattara magunguna da iskar Oxygen domin aikawa zuwa India.

Talla

A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter, shugabar Hukumar Tarayyar Turai , Ursula von der Leyen ta ce, sun shirya tsaf domin tallafa wa India da ke cikin mummunan hali a dalilin annobar Covid-19.

Ita ma Birtaniya ta ce, za ta aike da kayayyakin ceton-rai ga India da suka hada da injinan shakar iska ga marasa lafiya domin yaki da cutar ta Covid-19 bayan hukumomin New Delhi sun bukaci taimakon.

Amurka ta ce za ta taimaka wa kasar da kayayyakin lafiya da suka hada da na’urar taimaka wa marasa lafiya numfashi da kuma mahadan samar da rigakafi, amma fadar White House ba ta yi karin bayani ba kan ko za ta tsakuro wani adadi daga cikin alluran AstraZeneca milyan 30 da take ajiye da su.

Tuni gwamnatin India ta tsawaita dokar kulle a birnin New Delhi da mako guda sakamakon yadda coronavirus ta ta’azzara a kasar, inda a cikin sa’o’i 24, ta kashe mutane dubu 2 da 767 bayan ta harbi dubu 349 da 691.

Bidiyon cinkoson masu fama da cutar Korona da ke bukatar iskar Oxygen a asibitin India

Wannan adadi na rayukan da suka salwanta cikin kwana guda, shi ne mafi girma da India ta gani tun bayan bullar cutar.

A wani jawabin da ya saba gabatarwa ta kafar rediyo a duk wata, Firaministan India, Nerandra Modi ya ce, wata guguwa ta girgiza kasar, yana mai kira ga  mutanen kasar da su karbi allurar rigakafin cutar.

Gwamnatin India na shan caccaka

Ana ci gaba da  caccakar gwamnatin India saboda yadda ta bai wa al’umma damar gudanar da taruka daban-daban da suka hada da  bukukuwa na addini a sassan kasar a ‘yan makwannin nan, lamarin da ya kara ta’azzara yaduwar cutar Covid-19 a kasar mai yawan al’umma biliyan 1 da milyan 300.

Kawo yanzu wannan annoba ta Covid-19 ta kashe mutane sama da miliyan 3 a sassan duniya, yayin da India ta zama sabuwar cibiyar cutar.

Ana tara gawarwakin masu Korona a harabar asibitocin India domin kona su nan take.
Ana tara gawarwakin masu Korona a harabar asibitocin India domin kona su nan take. Gagan NAYAR AFP

Kasashen duniya sun kara kaimi wajen tsikara wa al'ummominsu allurar rigakafin cutar da zummar dakile yaduwarta, amma har yanzu akwai mutane da dama da ke dari-darin karbar allurar, abin da ya sa wasu ke ganin cewa, har yanzu akwai jan-aiki dangane da kawar da cutar daga doran-kasa.

Masana cutuka masu yaduwa irinsu Farfesa Kabir Sabitu na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a Najeriya sun ce, alfanun allurar rigakafin annobar sun fi rashin alfanunsu yawa.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da RFI Hausa ta yi da Farfesa Kabir Sabitu kan wannan batu

Hira kan alfanun rigakafin Korona tare da Farfesa Kabir sabitu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.