Isra'ila-Falasdinu

Human Right Watch ta zargi Isra'ila da nuna wariya ga Falasdinawa

Babban daraktan kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch Kenneth Roth.
Babban daraktan kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch Kenneth Roth. Johannes Eisele AFP/Archivos

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Right Watch ta zargi Isra’ila da nuna wariyar jinsi kan yankin Falasdinu zargin da ke biyo bayan tuhumar da kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ke yiwa kasar kan aikata laifukan yaki.

Talla

Kungiyar ta kare hakkin dan Adam, ta ce Isra’ilan ta tafka babban laifi wajen ci gaba da mamayar yankunan Larabawan falasdinu wanda ke nuna tsagwaron nuna wariya garesu, zargin da tuni Isra’ilan Yahudun ta musanta.

Human Right Watch wadda ta jima ta na zargin Isra’ilan a cutar ta Falasdinawa rahoton na ta a wannan karon na zuwa a wani yanayi da kotun ICC ke tsaka da tuhumar kasar ta Yahudu da zargin aikata laifukan yak ikan al’ummar yankin na Falasdinu.

Tuni dai Firaministan yankin na Falasdinu Mohammad Shtayyeh ya yi maraba da rahoton na Human Right Watch yana mai fatan rahoton ya budewa kasashen Duniya hanyar daukar mataki tare da tilastawa Isra’ilan amsa laifin cin zarafin da ta ke yiwa yankin.

Rahoton mai shafuka 213 ya bayyana yadda Isra’ila ta karbe iko yanzu haka da yankin da ke tsakankanin kogin Jordan da wani bangaren Mediterrannean  yayinda ta ke ci gaba da mamayar yammacin gabar kogin Jordan da zirin gaza da kuma birnin qudus da ta kwace iko da shi dukkaninsu da suka karya yarjejeniyar iyakokin bangarorin biyu ta 1948.

Kungiyar ta Human Right Watch ta ce manufofin Isra’ila na muzgunawa al’ummomin yankin na Falasdinu da suka kunshi ita kanta mamayar da kwace filaye mallakin ‘yan yankin da kuma hanasu takardar shaidar dan kasa da tilasta musu kaura ta hanyar sauya musu matsugunai baya ga take hakkokinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.