Amurka-Afrika

Sakataren wajen Amurka zai gana da shugabannin Najeriya da Kenya ta bidiyo

Sakataren wajen Amurka Antony Blinken.
Sakataren wajen Amurka Antony Blinken. ALEXANDER DRAGO POOL/AFP/Archivos

A yau talata sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai yi tattaunawa ta hoton bidiyo da shugabannin kasashen Najeriya da Kenya wata alama da ke nuni da muhimmancin da gwamnatin Joe Biden ke bai wa nahiyar Afirka.

Talla

Robert Godec, karamin sakataren wajen Amurka mai kula da nahiyar Afirka, ya ce bayan tattaunawa da Muhammadu Buhari da Uhuru Kenyatta ne Blinken zai ziyarci wani asibiti da kuma wata cibiyar samar da wutar lantarki da Amurka ta gina a Kenya, amma duk ta hoton bidiyo.

Ganawar ta Blinken tsakaninsa da shugabannin Najeriyar da Kenya na zuwa bayan yunkurin Nairobi don kulle sansanonin ‘yan gudun hijira na Kakuma da Dadaab da ke dauke da mutane fiye da dubu 400 galibinsu daga kasashen Somalia da Sudan ta kudu wadanda rikici ya rabasu da kasashensu.

A cewar Godec Amurka ta damu matuka da yunkurin na Kenya inda a tattaunawar ta hoton bidiyo tsakanin Blinken da Kenyata sakataren tsaron na Amurka zai sanar da matsayar kasarsa game da matakin.

Yayin ganawarsa da Muhammadu Buhari na Najeriya kuwa, da yiwuwar abubuwa masu alaka da tsaro su mamaye tattaunawar, dai dai lokacin da tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a kasar bayan harin boko haram da ya kashe sojin kasar 32 da kuma sace sace da kisan daliban jami'a a arewacin kasar.

A cewar Robert Godec da ke sanar da tattaunawar, Blinken ya zabi kasashen biyu na Kenya da Najeriya ne saboda doguwar alakar da ke tsakaninsu ta fuskar tsaro tattalin arziki, kasuwanci da kuma zuba jari tsawon shekaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.