Uruguay

Haɗiye ƙashin kifi ya tilastawa tsohon shugaban Uruguay kwanciya a asibiti

Tsohon shugaban kasar Uruguay José Mujica
Tsohon shugaban kasar Uruguay José Mujica Pablo PORCIUNCULA AFP/Archivos

Hadiye kashin kifi ya tilastawa kai tsohon shugaban kasar Uruguay Jose Mujico asibiti don a samu ayi masa fida a fitar da kashin.

Talla

Ma'aikatan asibitin kasar sunce shugaban mai shekaru 85 yanzu haka dai yana kwance, cikin wani hali amman kuma likitoci na cewa wani abu ne mai sauki yin fida a fitar da wannan kashin kifi, inda suke cewa watakila gobe ya koma gida.

Shi dai wannan tsohon shugaban kasa dai ya yi fice a zamanin mulkinsa tsakanin shekara ta 2010-2015, alokaci ko kadan baya karban albashi sai dai arabawa mabukata, sannan kuma tsohuwar motarsa da aka bar yayi, wato kirar Volkswagen Beetle yake hawa wanda a wani lokaci ya fitar da sanarwar cewar anyi tayin sayen motar tasa kan dala miliyan daya.

 Shugaban kasar da yafi talauci a duniya

Mr. Mujica wanda aka taba yi wa lakabi da "Shugaban kasar da ya fi kowane shugaba talauci" saboda yadda ya ke tafi da rayuwarsa, ya ce wani Balarabe ne ya yi masa tayin.

Ya kuma shaida wa wata mujallar kasar cewa idan har ya karbi kudaden to zai yi amfani da su ne wajen taimaka wa talakawa.

Shi dai shugaba Mujica wanda aka fi sani da Pepe yana zaune ne a wata sukurkutacciyar gona, kuma yana kyautar da kaso mafi yawa daga cikin albashinsa.

A shekarar 2010 ne ya bayyana dukiyarsa ta shekarar $1,800 wato daidai kudin da ya sayi motarsa Beetle a shekarar 1987.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.