IMF-CORONA

Mata sun fi wahaltuwa daga matsalar tattalin arzikin da Corona ta haddasa

Shugabar asusun bada lamuni na Duniya IMF Kristalina Georgieva .
Shugabar asusun bada lamuni na Duniya IMF Kristalina Georgieva . NICHOLAS KAMM AFP/File

Asusun bada lamuni na duniya IMF ya ce iyaye mata ne suka fi shan radadin matsalar tattalin arzikin da duniya ke fuskanta sakamakon annobar corona wadda ta mamaye duniya tun daga shekarar da ta gabata.

Talla

Shugabar asusun na IMF Kristalina Georgiva ta ce a bangaren gudanar da ayyukan yi, mata da kananan yara na daga cikin wadanda suka dandani kudar zaman gida da aka tilastawa jama’a a kasashe daban daban.

Binciken da Hukumar ta gudanar a kasashen Amurka da Birtaniya da kuma Spain ya nuna muhimmancin taimakawa matan wajen daukar dawainiyar kula da iyali maimakon sake musu komai.

Hukumar tace a kasar Amurka, mata sun fi maza shan wahala, yayin da a Birtaniya kuma maza ne suka fi mata shan wahala, sai Spain inda ake kan-kan-kan.

Rahotan ya ce, abin la’akari da shi shi ne iyaye mata a kasashen 3 sun fuskanci matsaloli sosai lokacin da hukumomi suka hana su fita domin yaki da annobar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.