G7 - China

G7 na shirin daukar mataki kan China

Taron ministocin wajen G7, a birnin London, ranar 4 ga watan Maris 2021
Taron ministocin wajen G7, a birnin London, ranar 4 ga watan Maris 2021 AP - Stefan Rousseau

Gungun kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya wato G7, sun shiga rana ta biyu a taron da suke yi a birnin London, inda a wannan talata suke kokarin samar da matsayi na bai-daya don tunkarar abin da suka kira barzanar aikin soji da ta kasuwanci da China ke yi wa duniya.

Talla

Mayar da hankali kan barazanar da kasar ta China ke yi wa duniya na matsayin amsa kiran da shugaban Amurka Joe Biden ya yi ne domin karfafa dimokuradiyya a duniya, inda aka gayyaci kasashen India,  Koriya ta Kudu da kuma Australia domin halartar taron da zai share tsawon kwanaki uku.

Taron ya kuma tattauna kan shirin nukilyar Iran da Koriya ta Arewa

Bayan da a ranar farko suka tattauna kan shirin nukilyar Iran da kuma Koriya ta Arewa, a yau ministocin harkokin wajen kasashen na nazari ne kan yadda ayyukan soji da na kasuwancin China ke matsayin barazana ga kasashen Yammacin Duniya da kuma dimokuradiyya.

‘’Ba wai manufarmu ba ce durkusar da kasar China’’ a cewar Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, inda ya ci gaba da cewa ‘’abin da muke nufi shi ne tabbatar da tsarin dimokuradiyya da muka jima muna ginawa a sassan duniya’’.

Shi kuwa takwaransa na Birtaniya Dominic Raab, kira ya yi ga China da ta mutunta alkawurran da ta dauka wa duniya ciki har da yarjejeniyar da aka kulla da ita a shekarar 1997 dangane da cikakken ‘yancin cin-gashin kan yankin Hong Kong.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.