Isra'ila-Zabe

Netanyahu na shirin sauka daga kujerar Firaministan Isra'ila

Benjamin Netanyahu na da wa'adin zuwa tsakar daren yau talata don kafa gwamnatin kawance.
Benjamin Netanyahu na da wa'adin zuwa tsakar daren yau talata don kafa gwamnatin kawance. EMMANUEL DUNAND AFP/Archivos

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce zai koma gefe tare da bai wa Naftali Bennett damar darewa kujerarsa a wata hadaka da ke da nufin hana masu sassaucin ra’ayi karbar ragamar jagorancin kasar ta Yahudawa.

Talla

Zuwa yanzu dai Naftali Bennett da ke matsayin tsohon na hannun daman Netanyahu kuma wanda ya zama mai fada a ji bayan zaben Isra’ilan na ranar 23 ga watan Maris da bai kammalu ba, bai fito karara ya bayyana amincewa da batun yarjejeniya ba.

Bayan da jam’iyyarsa ta Likud ta lashe akasarin kujerun majalisar dokoki a zaben, wanda shi ne na 4 a kasa da shekaru 2 da Isra'ilan ta gudanar, an bai wa Netanyahu wa’adin kwanaki 28 ya hada hadaka, wa’adin da zai cika da tsakar daren talatar nan.

Kafin Netanyahu ya iya kafa hadakar da ake bukata, dole sai ya cimma yarjejeniya da jam’iyyun Yahudawa masu sassaucin ra’ayi, da kuma jam’iyyar Raam ta Musulmai masu tsattsauran ra’ayi.

Netanyahu, wanda shi ne Firaministan Isra’ila da ya fi dadewa a karagar mulki, ana ganinsa a matsayin ummul aba'isin haddasa rarrabuwar kawuna a kasar.

Yanzu dai Firaministan mai shekaru 71 ya ce idan rabuwa da mulki zai bai wa jam’iyyarsa ta masu tsattsauran ra’ayi damar ci gaba da jagoranci a shirye ya ke ya sauka daga kujerarsa.

Acewar Netanyahu ya shaidawa Bennett cewa zai amince da bukatarsa ta mulkin karba karba, da zai ba abokin hamayyar nasa damar rike mukamin Firaminista na tsawon shekara guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI