Yunwa-Sauyin Yanayi

Karin mutane kusan miliyan 20 sun shiga bala'in yunwa a bara - Rahoto

Yankin Matam dake arewa maso gabashin kasar Senegal da fari ko kwararowar hamada ke yiwa barazana.
Yankin Matam dake arewa maso gabashin kasar Senegal da fari ko kwararowar hamada ke yiwa barazana. AP - Rebecca Blackwell

Hukumar hadin gwiwar kasashe domin yaki da yunwa ta ce an samu karin kusan mutane miliyan 20 da suka fuskanci bala’in na yunwa a fadin duniya cikin shekarar bara.

Talla

Cikin rahoton da ta saba fitarwa duk shekara, hukumar ta bayyana tashe-tashen hankula, matsalar sauyin yanayi da kuma annobar Korona a matsayin manyan dalilan da suka jefa miliyoyin mutanen cikin kangin yunwa.

Hukumar dake karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar turai EU tun bayan kafuwarta a shekarar 2016, ta kara da gargadin cewar matsalar karancin abinci na cigaba da yin muni tun daga shekarar 2017 har zuwa wannan lokaci, kuma babu alamun za a samu sassauci ko a wannan shekarar saboda matsalolin na tashe-tashen hankula da kuma tasirin annobar Korona.

Wasu 'yan kasar Senegal dake yankin Matam a arewa maso gabashin kasar.
Wasu 'yan kasar Senegal dake yankin Matam a arewa maso gabashin kasar. AP - Rebecca Blackwell

A Jumlace dai akalla mutane miliyan 155 suka fuskanci bala’in yunwa cikin shekarar bara a sassan duniya, adadi mafi yawa da rahoton hukumar hadin gwiwar kasashe mai yaki da yunwa ya bayyana cikin shekaru 5.

Rahoton ya kara da cewar akalla mutane 2 cikin kowadane 3 da yunwa ta tagayyara a Africa suke, yayin da kuma Yemen, Afghanistan, Syria da Haiti ke cikin kasashe 10 da matsalar yunwar tafi muni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI