MDD-Hakkin dan Adam

Kasashe mambobin MDD na kan gaba wajen take hakkin dan Adam- rahoto

China na jerin kasashe 'yan gaba gaba da suka yi kaurin suna wajen take hakkin bil'adama.
China na jerin kasashe 'yan gaba gaba da suka yi kaurin suna wajen take hakkin bil'adama. AP - Aaron Favila

Wani rahoton hukumar sa ido kan kare hakkin dan adam ta kasa da kasa ISHR, ya samu hukumomin kusan rabin kasashen da ke karkashin hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya, da laifin cin zarafi ko yin barazana ga lauyoyi da sauran jami’ai masu fafutukar kare hakkin dan adam.

Talla

Sabon rahoton ya ce hukumar ta ISHR ta tattara hujjojinta ne daga korafe-korafe 709 da ta samu a tsakanin shekarun 2010 zuwa 2020, inda lauyoyi da sauran masu fafutukar da ke taimakawa majalisar dinkin duniya wajen fallasa rahotannin cin zarafin dan adam suka fuskanci matsaloli daga hukumomin kasashen da su ke, da suka hada da barazana ga raukansu, azabtarwa, bata suna, dauri ba bisa ka’ida ba, da kuma haramta musu tafiye-tafiye.

A halin yanzu Bahrain ke kan gaba tsakanin kasashen da suka fi cin zarafin lauyoyi da sauran jami’ai masu faufutukar kare hakkin dan adam bayan samun korafe-korafe 64 cikin shekaru 10, Venezuela ke biye a matsayin ta biyu, sai China da kuma Masar.

Sai dai masu bincike sun yi gargadin akwai yiwuwar adadin masu fafutukar kare hakkin na dan adam da ake cin zarafinsu a sassan duniya ya zarta na alkaluman da aka tattara, musamman a kasashen da hukumomi ke takurawa kungiyoyin fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI