Lafiya

MDD ta koka kan karancin unguwarzoma a sassan duniya

Blandine Mekpo, wata unguwarzoma yayin yiwa mata masu juna biyu karin bayani kan cutar AIDS a garin Bohicon dake kudancin Jamhuriyar Benin.
Blandine Mekpo, wata unguwarzoma yayin yiwa mata masu juna biyu karin bayani kan cutar AIDS a garin Bohicon dake kudancin Jamhuriyar Benin. AFP/Getty Images - DELPHINE BOUSQUET

Hukumar Lafiya ta Duniya tace ana bukatar akalla karin unguwarzoma 900,000 akan wadanda ake da su yanzu domin ceto rayuwar mata masu ciki da ‘yayan dake cikin su a fadin duniya.

Talla

Hukumar tace karancin wadannan masu aikin lafiya na matukar illa ga miliyoyin mata da ‘yayan dake cikin su, yayin da wasu miliyoyi ke fuskantar rashin lafiya da rashin kular da ake bukata abinda ke kaiga rasa rayukan wasu daga cikin su.

Hukumar tace zuba jari wajen kara yawan wadannan ma’aikatan lafiya nan da shekarar 2035 zai taimaka wajen ceto rayuwar mata akalla miliyan 4 da rabi kowacce shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.