Duniya - Hakkin Yara

SOS ta soma bincike kan tuhumar ma'aikatanta da cin zarafin yara

Hoto domin misali dake nuna wasu kananan yara
Hoto domin misali dake nuna wasu kananan yara © Reuters/File

Kungiyar agaji ta kasa da kasa SOS, ta bayyana kaddamar da bincike domin tabbatar da gaskiya kan zargin yadda ma’aikatan ta ke cin zarafin yaran dake karkashin kulawar ta a kasashen Afirka da Asia.

Talla

Shugabar kungiyar SOS International dake kula da yara akalla miliyan guda da dubu 200 a kasashen duniya, Elizabeth Hauser tace gudanar da binciken ya zamo wajibi domin kauda duk wani shakku kan zargin da ake yiwa ma’aikatan ta na cin zarafin yaran da aka basu amana.

Jami’ar tace wannan korafe korafen sun fito ne daga kasashe 20 daga cikin kasashe 137 da take aiki a cikin su, kuma sun hada da karkata akalar kudaden tafiyar da gidajen kula da yaran da kuma cin zarafin su ta hanyoyi daban daban.

Hauser tace akwai zargin cewar wasu daga cikin shugabannin wannan kungiyar suna da labarin abinda ke faruwa amma ba su dauki mataki ba.

Ita dai kungiyar na da cibiyoyi sama da 550 a kasashe da dama da take gudanar da harkokin ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.