Iran-Nukiliya

An soma taro kan makomar yarjejeniyar nukiliyar Iran zango na 4

Kazem Gharib Abadi babban jakadan Iran a hukumar sa ido kan makamashin nukiliya ta duniya.
Kazem Gharib Abadi babban jakadan Iran a hukumar sa ido kan makamashin nukiliya ta duniya. AP - Lisa Leutner

Wakilan manyan kasashen duniya da na Iran sun soma taron kan makomar yarjejeniyar Nukiliyar kasar karo na 4 yau Juma’a a birnin Veinna, cike da fatan cimma matsayar kan komawar Amurka cikin yarjejeniyar da kuma sansanta ta da Iran.

Talla

Wakilan manyan kasashen da har yanzu ke cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shekarar 2015 da suka hada da China, Birtaniya, Faransa, Jamus da Rasha da kuma kasar ta Iran sun gana tasawon akalla sa’a guda a babban birnin kasar Austria, inda jakadan majalisar dinkin duniya a birnin na Vienna Mikhail Ulyanov ya bayyana kwarin gwiwar cimma nasarar da suke nema.

Taron da aka soma dai ya maida hankali ne kan bukatar Iran na janye dukkanin takunkuman da tsohon shugaba Trump ya kakaba mata, da kuma gamsar da Iran din ta koma mutunta yarjejeniyar nukiliyar da ta soma bijirewa.

Jakadan Rasha a hukumar sa ido kan makamashin nukiliya ta duniya IAEA Mikhail Ulyanov, yayin taron manema labarai a birnin Vienna kan makomar yarjejeniyar nukiliyar Iran.
Jakadan Rasha a hukumar sa ido kan makamashin nukiliya ta duniya IAEA Mikhail Ulyanov, yayin taron manema labarai a birnin Vienna kan makomar yarjejeniyar nukiliyar Iran. AP - Lisa Leutner

Dukkanin jami’an Dilflomasiyar dake halartar taron zagaye na 4 kan makomar nukiliyar ta Iran dai sun bayyana fatan ganawar ta zama ta karshe kan aniyar sake karfafa yarjejeniyar nukiliyar, wadda sannu a hankali ta rika sakwarkwacewa tun bayan da tsohon shugaba Donald Trump ya janye Amurka daga cikinta a shekarar 2018, yayin da Iran ta maida raddin bijirewa wasu daga cikin sassan yarjejeniyar.

Sai dai sabon shugaban Amurka Joe Biden ya yi alkawarin komawa cikin yarjejeniyar nukiliyar, matakin da wani jami’in diflomasiyar kasar ya ce za a iya cimma nan da ‘yan makwanni kafin gudanar zaben shugabancin kasar Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI