Falasdinawa - Isra'ila

Mutane fiye da 200 sun jikkata dalilin arangama a Masallacin Kudus

Wasu Falasdinawa da 'yan sandan Isra'ila suka harbawa barkonon tsohuwa a birnin Kudus.
Wasu Falasdinawa da 'yan sandan Isra'ila suka harbawa barkonon tsohuwa a birnin Kudus. AP - Maya Alleruzzo

Falasdinawa akalla 205 tare da ‘yan sandan Isra’ila 17 ne suka jikkata sakamakon wata arangama da bangarorin biyu suka yi a Masallacin Al-aqsa.

Talla

Jami’an hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda Waseem Bader ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillacin labarai na AFP.

Waseem ya ce lamarin ya kazanta ne bayan da jami’an tsaro suka yi amfani da karfin da ya wuce kima kan masu zanga-zanga da suka rika jifan jami’an tsaron da duwatsu da kwalabe.

Wani dan sandan Isra'ila yayin kokarin korar Falasdinawa daga wurin da rikici ya barke a Masallacin Kudus.
Wani dan sandan Isra'ila yayin kokarin korar Falasdinawa daga wurin da rikici ya barke a Masallacin Kudus. AP - Maya Alleruzzo

Rikicin da ya tashi zanga-zangar ya fara ne a juma’ar makon jiya bayan da rashin fahimtar da ta shiga tsakanin Falasidnawa da wasu Yahudawa.

Sabon rikicin tsakanin Falasdinawa da daruruwan ‘yan sandan Isra’ila na zuwa ne a dai dai lokacin da zaman tankiya ke karuwa tsakanin bangarorin saboda shirin gwamnatin Isra’ila na mamaye karin yankunan Falasdinawa a gabashin birnin Kudus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.