Iraqi - Zanga-zanga

Zanga-zanga ta barke a Karbala bayan kashe wani fitaccen mai fafutuka

Masu zanga-zanga a birnin Karbala na kasar Iraqi.
Masu zanga-zanga a birnin Karbala na kasar Iraqi. © | AFP

Zanga-zanga ta barke a birnin Karbala dake kasar Iraqi biyo bayan kashe Ihab al-Wazni wani mai fafutuka da yayi kaurin suna wajen sukar gwamnati, lamarin da ya fusata dubban magiya bayansa da suka fantsama kan titunan don nuna bacin ransu.

Talla

Wasu ‘yan bindiga haye kan babura suka harbe shi har lahira, harin da na’urorin daukar hoto suka nada.

Ko a watan Disambar shekarar 2019 sai da ta wazni ya tsallake rijiya da baya, lokacin da wasu ‘yan bindigar suka suka kashe wani abokinsa Fahem al-Tai mai fafutuka, a dai dailokacin da yake ajiye shi gida a birnin Karbala.

Kawo yanzu kimanin masufafutukar kare hakkin dan adam 30 aka kashe yayin da aka sace wasu da dama daga watan Oktoban 2019 zuwa bana a Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI