Falasdinawa - Yuhudawa

Dakarun Hamas sun tabbatar da hallaka wasu sojojin Isra'ila

Hayaki dake tashi bayan harin Isra'ila a Gaza, 2 ga watan Mayu 2021
Hayaki dake tashi bayan harin Isra'ila a Gaza, 2 ga watan Mayu 2021 MOHAMMED ABED AFP

Hukumomin Gaza sun tabbatar da hallaka wasu sojojin Israe’la bayan da suka harba rokoki, dai-dai kan iyakar yankin da Isra’ilan, a wani abu mai kama da ramuwar gayya.Tun makon da ya gabata dai rikici ke kara tsananta kusan kowacce rana, inda kasashen biyu ke harba makaman rokoki a tsakanin su, abinda ya yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa 56 da kuma yahudawa 6.

Talla

Ya zuwa yanzu dai yahuwada 100 sun jikkata, a yayin da Falasdinawa kusan 250 ke kwance a gadon asibiti, sakamakon yadda ake musayar harba makamai a tsakanin juna.

Hamas

Itama kungiyar Hamas ta ce manyan kwamandojin ta da dama sun rasa rayukan su sakamakon hari ta sama da sojojin Isra’ila suke kaiwa yankin, cikin su kuwa har da babban kwamandan ta Bassem Issa.

Masu makoki dauke da gawar Majd Abu Saadahthe, ba Falasdine da da Isra'ila ta hallaka a yankin Gaza
Masu makoki dauke da gawar Majd Abu Saadahthe, ba Falasdine da da Isra'ila ta hallaka a yankin Gaza SAID KHATIB AFP

Da yake jawabi bayan kisan Frime ministan Isra’ila Benjamin Natenyahu, ya ayyana kisan babban kwamandan a matsayin nasara, yana mai gargadi kan cewa rayukan Falasdinawa na cikin hadari.

Zamu ci gaba da yiwa Isra'ila luguden wuta

Sai dai kuma da take mayar da martani, kungiyar Hamas ta ce dakarunta sun shirya tsaf don yiwa sojojin Isra’ila luguden wuta.

Baya ga kisan sojojin Isra’ilan da suka mutu, Hamas ta kuma ce ta jikkata wani sojan Isra’ila daya.

Dakarun Isra'ila dake luguden wuta kan Falasdinawa 12 ga watan Mayan 2021.
Dakarun Isra'ila dake luguden wuta kan Falasdinawa 12 ga watan Mayan 2021. AFP - HAZEM BADER

Sojojin Gaza sun harba makaman roka zuwa Isra’ila sama da dubu 1 tun daga ranar litinin din makon jiya zuwa yanzu kamar yadda rundunar sojan Isra’ilan ta bayyana, sai dai itama ta ce ta hallaka manyan kwamandojin Hamas din da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.