Falasdinawa-Isra'ila

MDD za ta fara zama kan rikicin Falasdinawa da Isra'ila a makon gobe- Amurka

Wani yanki da hare haren Isra'ila ya shafa a Gaza.
Wani yanki da hare haren Isra'ila ya shafa a Gaza. REUTERS - SUHAIB SALEM

Amurka ta nuna goyon baya ga shirin Majalisar Dinkin Duniya na gudanar da zama na musamman kan rikicin da ya barke tsakanin Isra’ila da yankin Falasdinu, dai dai lokacin da jami’an diflomasiyya ke ganin Washington ce ta yi karfa karfa wajen hana taron a gobe Juma’a.

Talla

Sakataren wajen Amurkan Antony Blinken ya bayyana cewa kasar na goyon bayan taron kwamitin tsaro na Majalisar, sai dai zuwa makon gobe za a iya samun damar tunkarar rikicin ta fuskar Diflomasiyya gabanin hukuncin Majalisar.

A wata zantawarsa da manema labarai, Blinken ya jaddada aniyar Amurka ta tabbatar da zaman lafiyan gabas ta tsakiya.

Zuwa yammacin yau Alhamis Falasdinawa 100 Sojin Isra’ila suka hallaka a rikicin yayinda wasu daruruwa kuma suka sake jikkata kari kan wadanda ke raunata kowacce rana tun bayan farowar rikicin kwanaki 6 da suka gabata.

Sojin Saman Isra’ila ne ke ci gaba da amfani da jiragen yaki wajen kaddamar da farmaki kan Falasdinawan bisa fakewa da yakar Sojin Hamas kungiyar da ke rike da makami a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI