Isra'ila - Falasdinawa

Luguden wuta a kan Gaza ya hallaka akalla mutane 120 tare da jikkata 830

Isra'ila ta ci gaba da luguden wuta a kan Zirin Gaza
Isra'ila ta ci gaba da luguden wuta a kan Zirin Gaza AFP - SAID KHATIB

Isra’ila ta ci gaba da luguden wuta ta sama da kasa a kan Gaza a matsayin martani ga hare-haren da mayakan Hamas ke tsananta kai wa da rokoki da manya- manyan bindigogi a kan yankunan Yahudawa, lamarin da ya ta’azzara rikicin da ya lakume rayuka sama da 120.

Talla

Rundunar sojin Isra’ila ta ce hare-haren da ta kaddamar cikin dare sun hada da na jiragen yaki da tankuna a kan wata hanyar bututun karkashin kasa da Hamas ta gina a yankunan fararen hula, sai dai ta ce a wannan karon ba ta samu damar ankarar da fararen hula kamar yadda ta yi gabanin hare – haren da ta kaddamar a hasumiyar Gaza a makon da ya gabata ba.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa  gidaje da dama a yankunan Gaza da ke da yawan jama’a ne suka salwanta, a yakin da ministan Lafiyar Gaza ya ce yanzu haka ya lakume rayukan Falasdinawa 119 ciki har da yara 31, ya kuma raunata 830.

Wata mata, Ba-Yahudiya, wacce ta zarce shekaru 80 da haihuwa ta rasu a cikin daren Alhamis sakamakon raunukan da ta samu a yayin da take neman mafaka daga rokokin da ake harbawa, abin da ya kawo adadin mamata a bangaren Isra’ila 8, ciki har da wani yaro mai shekaru 6, da soja daya.

Sama da rokoki dubu 1 da 800 ne mayakan Hamas suka harba Isra’ila, akasari a biranen kudancin kasar, amma kuma har da Tel Aviv da Jerusalem.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.