WHO-Coronavirus

Annobar Coronavirus za ta tsananta a wannan shekarar

Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus. AP - Salvatore Di Nolfi

Hukumumar lafiya ta duniya ta yi gargadi a jiya Juma’a cewa annobar Korona za ta yi tsanani a shekararta ta 2, a yayin da Japan ta fadada dokar ta baci a tsakankanin kiran da ake cewa a soke gasar Olympic.

Talla

Lamarin ya tsananta a Japan inda hukumomi suka fadada dokar ta-baci da suka  sanya a dalilin annobar   zuwa yankuna 3, makonni 10 kafin fara gasar  wasannin motsa jiki ta Olympic, a yayin da masu adawa da gudanar da gasar suka mika wasika neman soke ta maai dauke da sa hannun sama da mutane dubu 300 da 50.

A yayin da  Tokyo da sauran Yankuna ke karkashin dokar ta-baci har zuwa karshen watan Mayu, Hiroshima, Okayama da arewacin Hokkaido, inda za a gudanar da wasannin tsere za su bi sahu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.