Isra'ila - Falasdinawa

Isra'ila ta raba Falasdinawa dubu 10 da muhallansu - MDD

Wasu Falasdinawa yayin jimamin muhallansu da Isra'ila ta rusa a birnin Gaza. 14/5/2021.
Wasu Falasdinawa yayin jimamin muhallansu da Isra'ila ta rusa a birnin Gaza. 14/5/2021. © REUTERS/Mohammed Salem

An shiga rana 6 a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa kan Falasdinawa a zirin Gaza, inda a yau asabar barin wutar jiragen yakin Isra’ilar ya kai ga kashe mutane 10 cikinsu har da kananan yara 8 a wani sansanin ‘yan gudun hijira.

Talla

Farmakin Isra’ilar ya kuma rusa gine-ginen da suka kunshi ofisoshin kamfanin dillancin labarai na AP da kuma kafar talabijin ta Aljazeerah.

Kawo yanzu akalla Falasdinawa 140 suka mutu cikin har da yara kanana 39, yayin da wasu kimanin 950 suka jikkata, tun bayan kaddamar da hare-haren da Isra’ila tayi kan birnin Gaza a ranar litinin da ta gabata.

Wasu mata Falasdinawa a harabar gidajen da jiragen yakin isra'ila suka rusa a birnin Gaza.
Wasu mata Falasdinawa a harabar gidajen da jiragen yakin isra'ila suka rusa a birnin Gaza. © REUTERS/Mohammed Salem

A gabar yamma da kogin Jordan kuwa rahotanni sun ce jami’an tsaron Isra’ila sun kashe Falasdinawa akalla 13, yayin arrangamar da suka yi da Falasdinawan dake zanga-zanga kan neman dakatar da hare-haren da aka kaddamar kan birnin Gaza.

A bangaren Isra’ila kuwa, ta ce akalla mutane  9 mayakan Hamas suka kashe mata, sakamakon daruruwan rokokin da suka harbawa kan wasu biranen ta daga Gaza.

Majalisar dinkin duniya ta kiyasata cewar Falasdinawa dubu 10 sun rasa muhallansu dalilin rikicin da ya barke a makon jiya, tare da bayyana fargabar tagayyar da fararen hular suka yi ka iya fin haka muni a nan gaba kadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI