Jamus - Falasdinawa

Jamus ta yi Allah-wadai da matakin Hamas na harba rokoki kan Isra'ila

Kakakin gwamnatin Jamus Steffen Seibert.
Kakakin gwamnatin Jamus Steffen Seibert. AP - Michael Sohn

Kasar Jamus ta kwatanta harba rokokin da kungiyar Hamas ke yi zuwa Isra’ila a matsayin ta’addanci la’akari da rikicin da ke faruwa yanzu haka a yankin gabas ta tsakiya.

Talla

Jami’in yada labaran shugabar gwamnatin kasar Angela Markel, Steffen Seibert ya ce kungiyar ta Hamas ba ta da wani buri illa ta halaka mutane, da kuma sanya fargaba a zukatan jama’a.

A cewar ta babu abinda Isra’ila ke yi sai kokarin kare kanta, daga hare-haren roka da Hamas ke jefawa kan Isra’ila.

Rikicin kasashen biyu ya faro ne tun ranar litinin din makon jiya daga masallacin Al Aqsa, biyo bayan matakin Isra’ila na kokarin mamaye wasu karin yankunan Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI