Isra'ila - Falasdinawa

Luguden wuta da Isra'ila ke yi a kan Gaza ya halaka mutane 10 'yan iyali guda

Falasdinawa na makokin mutuwar mutane 10 'yan iyali guda da hare haren Isra'ila suka kashe.
Falasdinawa na makokin mutuwar mutane 10 'yan iyali guda da hare haren Isra'ila suka kashe. MAHMUD HAMS AFP

Ma’aikatan lafiya a yankin Falasdinawa sun ce mutane 10 daga iyali guda sun gamu da ajalinsu a safiyar Asabar dinnan biyo bayan luguden wuta da sojin saman Isra’ila suka yi a yankinsu.

Talla

‘Yaya 8 da mata 2, duk daga iyalin Abu Hatab sun mutu a wani bene mai hawa 3, da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Shati da ya ruguje bayan harin da Isra’ila ta kai.

Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare a wasu wurare a yankin Zirin Gaza a cikin dare, kwana guda bayan mummunan luguden wuta a  yankin Yamma da Tekun Jordan  a yayin da adadin wadanda suka mutu ke dada   karuwa.

Duk da kokarin da kasashen duniya ke yi na kwantar da hankula a rikicin da aka shafe kwanaki 5 ana yi tsakanin Israila da mayakan Hamas a yankin, sojin saman Isra’ilar sun yi ta luguden wuta  a cikin dare, a yayin da  kungiyar Hamas ke ci gaba da aikewa da rokoki zuwa yankin Yahudawa.

Adadin wadanda suka mutu a yankin na Gaza ya kai 126, ciki har da yara 31, a yayin da ya zuwa yanzu wadanda suka jikkata sun kai 950.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.