Isra'ila-Falasdinu

An tashi baram-baram yayin zama kan rikicin Falasdinawa da Isra'ila a MDD

Yadda Isra'ila ke ci gaba da rugurguza yankin Gaza ta hanyar yi mata luguden makaman roka.
Yadda Isra'ila ke ci gaba da rugurguza yankin Gaza ta hanyar yi mata luguden makaman roka. AFP - ANAS BABA

Jiragen yakin Isra’ila sun kwashe daren jiya suna lugugen wuta a kan zirin Gaza, inda alkaluma ke nuni da cewa akalla Palasdinawa 42 ne suka rasa rayukansu a cikin sa’o’I 24 na baya-bayan nan, adadin mafi yawan a rana daya tun bayan barkewar rikicin.

Talla

Wannan dai na zuwa a daidai lokacin da karo na biyu Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya tashi baram-baram ba tare da cimma wata matsaya dangane da wannan rikici ba, yayinda China ta zargi Amurka da haddasa tarnaki ga yunkurin kasashen duniya na samar da matsayi na bai-daya a taron da aka gudanar jiya lahadi.

Taron da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar a jiya lahadi ya kasance dama ga wakilan kasashe 15 mambobi don kowanne ya bayyana matsayinsa, inda a jawabinsa na bude taron babban magatakardar Majalisar Antonio Guterres ya bukaci a tsagaita wuta tun kafin rikicin ya haifar da sabuwar matsala ga ayyukan jinkai a duniya.

Ministan harkokin wajen China Wang Yi, ba tare da yin wata rufa-rufa ba, ya zargi Amurka da haddasa tarnaki karo na biyu ga yunkurin da kasashen Duniya ke yi don fitar da sanarwar ta bai-daya dangane da wannan rikici, yayin da jakadiyar Amurka a majalsiar Linda Thomas-Greenfield ta kare matsayin kasar a lokacin wannan mahawara.

Shi kuwa Ministan harkokin wajen Palasdinu Riyad Al-Maliki, zargin Isra’ila ya yi da afka wa al’ummar Palasdidu tare da lalata wuraren ibadarsu, yana mai kira ga kasashen duniya da su yarda cewa Isra’ila ta aikata laifufukan yaki da kuma cin zarafin bil’adama a yankin.

To sai dai jakadan Isra’ila a Majalisar ta Dinkin Duniya Glad Erdan, nan ta ke ya mayar da martani ta hanyar zargin kungiyar Hamas da tayar da wannan rikici dagangan domin samun karbuwa da kuma karbe madafan iko a Gabar Yammacin Kogin Jordan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI