Isra'ila - Falasdinawa

Isra'ila ta kaddamar da sabbin hare-hare kan zirin Gaza

Wani gini da jiragen yakin Isra'ila suka kaiwa farmaki a birnin Gaza. 17/05/2021.
Wani gini da jiragen yakin Isra'ila suka kaiwa farmaki a birnin Gaza. 17/05/2021. AP - Hatem Moussa

Sojojin Isra’ila sun kaddamar da wasu jerin hare-hare ta sama kan zirin Gaza da safiyar yau Litinin, sa’o’i bayan da Fira Ministan Isra’ilar Benjamin Netanyahu sha alwashin cigaba da kaiwa yankin Falasdinawan farmaki har sai abinda hali yayi.

Talla

Sabbin hare-haren jiragen yakin Isra’ilar dai sun haifar da rugugin fashe-fashen da suka girgiza sassan arewaci da kuma kudancin birnin Gaza, hare-haren da wadanda suka shaida su suka ce sun zarta na ranar Lahadi, inda Falasdinawa akalla 42 suka mutu tare da jikkatar wani.

Zuwa yanzu Falasdinawa akalla 198 cikinsu har da kananan yara 58, sojojin Isra’ila suka kashe, tare da jikkata wasu fiye da dubu 1 da 300, tun bayan kaddamar da hare-haren da suka yi kan zirin Gaza mako guda da ya gabata.

Wani titi da hare-haren jiragen yakin Isra'ila suka ragargaza a birnin Gaza.
Wani titi da hare-haren jiragen yakin Isra'ila suka ragargaza a birnin Gaza. AP - Hatem Moussa

A bangaren mayakan Falasdinawa na Hamas kuwa kawo yanzu makaman roka kimanin dubu 3 da 100  suka harba kan wasu biranen Isra’ila, inda hukumomin kasar suka tabbatar da mutuwar mutane 10 cikinsu yara 2.

Jiya Lahadi kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar da taro kan tashin hankalin da ake ciki a birnin Gaza, amma kwamitin ya gaza fitar da sanarwar matsayar da ya cimma akai, laifin da China ta dora kan Amurka da tace ita ta ta hana fitar da sanarwar bayan taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI