Isra'ila - Falasdinawa

Kwamitin sulhun MDD zai sake zama kan rikicin Isra'ila da Falasdinawa

Yadda jiragen yakin Isra'ila suka cigaba da kai hare-haren kan birnin Gaza a daren ranar Litinin. 17/5/2021.
Yadda jiragen yakin Isra'ila suka cigaba da kai hare-haren kan birnin Gaza a daren ranar Litinin. 17/5/2021. AFP - ANAS BABA

Isra’ila ta cigaba da kai hare-hare kan sassan zirin Gaza, inda a daren jiya ta rusa karin gine-gine ciki har da cibiyar gwajin gano cutar Korona guda da birnin ya mallaka.

Talla

Yau Talata ne dai kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya zai sake zama a karo na 4 kan kazancewar rikicin na Isra’ila da Falasdinawa.

Tun a ranar 10 ga watan Mayun da muke Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta sama kan birnin Gaza, bayan da mayakan Hamas suka harba mata makaman roka, sakamakon barkewar rikici a Masallacin Al Aqsa dake birnin Kudus tsakanin ‘yan sandan Isra’ila da Falasdinawa masu zanga-zangar adawa da mamaye karin yankunansu da Isra’ila ke yi a birnin.

Hare-haren jiragen yakin Isra'ila kan birnin Gaza.
Hare-haren jiragen yakin Isra'ila kan birnin Gaza. MAHMUD HAMS AFP

Tun bayan barkewar yakin dake zama mafi muni da aka gani a shekarun baya bayan nan, Falasdinawa 212 suka rasa rayukansu ciki har da yara 61, wasu fiye da dubu 1 da 400 kuma suka jikkata, sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kaddamar. A Isra’ila kuwa mutane 10 suka mutu ciki har da yara , wasu daruruwa kuma suka jikkata saboda hare-haren dubban makaman rokar da mayakan Hamas ke harbawa sassan kasar.

Yadda mayakan Falasdinawa na kungiyar Hamas ke harba makaman roka kan Isra'ila daga birnin Gaza.
Yadda mayakan Falasdinawa na kungiyar Hamas ke harba makaman roka kan Isra'ila daga birnin Gaza. AP - Hatem Moussa

Tsanantar rikicin ya sanya kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya shirin zama a yau Talata, taron dake zama karo na 4 a tsawon mako 1.

A jiya Litinin Amurka karo na uku jere a mako 1, ta kada kuri’ar kin amincewa da fitar da sanawar hadin gwiwar manbobin kwamitin sulhun da zummar kira ga bangaren Isra’ila da na Falasdinawa kan su dakatar da kaiwa juna hare-hare, sai dai shugaban Joe Biden ya shaidawa Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu yana goyon bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI