Isra'ila-Falasdinu

Bai wa Falasdinu kasa mai 'yanci shi zai warware rikicinsu da Isra'ila - Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi na'am da tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.
Shugaban Amurka Joe Biden ya yi na'am da tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas. Nicholas Kamm AFP

Shugaban Amurka Joe Biden ya sha alwashin taiamakawa wajen sake gina Gaza, yana mai cewa samar da kasar Falasdinawa da za ta wanzu da ta Isra’ila ce hanya daya tilo ta kawo karshen rikicin yankin.

Talla

Sai dai ya ce babu ja da baya a game da  kudirinsa na tabbatar da tsaron Isra’ila, inda ya kara da cewa idan ba yankin ya amince da wanzuwar Isra’iala matsayin kasa ba, zaman lafiya zai yi wuyar samuwa.

Ya ce batun samar da kasashe biyu, na Falasdinawa da Isra’ila, da Birnin Kudus a matsayin babban birninsu, ya kasance mahimmin abu a cikin gwamman shekaru na diflomasiyar kasa da kasa, a kokarin da ake na kawo karshen rikicin Falasdinu da Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.