Falasdinawa - Isra'ila

Dubban mutane sun yi zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa a Faransa

yadda hare-haren isra'ila suka barnata gine-gine a Gaza.
yadda hare-haren isra'ila suka barnata gine-gine a Gaza. AFP - EMMANUEL DUNAND

Dubban mutane ne a yau Asabar sun gudanar da zanga-zangar lumana a birnin Paris da wasu garuruwan kasar Faransa domin nuna goyan bayansu ga Falasdinawa bayan kawo karshen kwanaki 11 ana rikici tsakanin su da Israila wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 260.

Talla

Bertrand Hellbronn, shugaban kungiyar da ke goyan bayan Falasdinawa ya ce tsagaita wuta ba zai magance rikicin ba, domin kuwa rikicin ya shafi duk wani mai goyan bayan ganin an aiwatar da gaskiya da mutunci da kuma doka.

Masu zanga-zangar a Paris sun yi ta ihu suna cewa F‘alasdinu zata yi nasara’, ‘Israila na kashe jama’a.

Kungiyar ma’aikatan Faransa ta CGT ta ce akalla mutane 4,000 suka shiga zanga-zangar ta birnin Paris.

Wani matashi mai shekaru 28, Wael ya ce ko da an kawo karshen harin bama baman, 'yan kama- wuri -zauna- suna nan. Mazauna Sheikh Jarrah na ci gaba da fuskantar kora kuma yankin Gaza na ci gaba da fuskantar mamaya.

Rahotanni sun ce an gudanar da irin wannan zanga-zanga a birnin Strasbourg da Lille da Toulouse da Montpellier.

Imad Deaibis da ke Strasbourg ya ce Falasdinawa na da hakkin rayuwa cikin kwanciyar hankali amma kasar Israila ta hana su ‘yancinsu da gidajensu.

Deaibis ya ce shi Bafalasdine ne amma ba shi da ‘yancin zuwa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.