G7 - Canjin Yanayi

Kasashen G7 za su daina tallafawa masana'antu masu amfani da makamashin Kwal

Yadda hayaki ke fita daga wata masana'atar dake amfani da makamashin Kwal a birnin Belgrade dake kasar Serbia.
Yadda hayaki ke fita daga wata masana'atar dake amfani da makamashin Kwal a birnin Belgrade dake kasar Serbia. © REUTERS/Marko Djurica

Kungiyar kasashen G7 mafiya karfin tattalin arziki, sun cimma matsayar kawo karshen goyon baya, ko samar da kudaden tafiyar da ayyukan cibiyoyi ko kamfanonin da suke amfani da makamashin Kwal nan da zuwa karshen shekarar da muke ciki.

Talla

Kasashen na G7 sun kuma yi alkawarin tsaurara matakan yaki da fitar da gurbatacciyar iskar carbon a yayin da ake kokatin samar da makamashin hasken lantarki nan da shekarar 2030.

Yayin da suke shirin gudanar da taronsu na gaba a Birtaniya cikin wata mai kamawa ministocin kula da Muhalli da na kasashen na G7, sun jaddada alwashin daukar matakan dakile dumamar yanayi ta hanyar tabbatar da cewar karuwar zafin yanayin yayi kasa da maki 1.5 a ma’aunin Celcius.

Ministocin sun bayyana haka ne yayin ganawar da suka yi ta kafar bidiyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI