Falasdinawa - Isra'ila

Amurka ta jaddada bukatar kafa kasar Falasdinu

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken. AP - Andrew Harnik

Kasar Amurka ta sake jaddada matsayin ta na ganin an kafa kasar Falasdinu da zata zauna kafada da kafada da kasar Israila a matsayin hanya daya tilo da zata tabbatar da zaman lafiya tsakanin Israila da Falasdinu.

Talla

Sakataren harkokin wajen kasar Antony Blinken ya bayyana haka bayan gwabzawar da akayi tsakanin bangarorin biyu na kwanaki 11 wanda yayi sanadiyar kasha Falasdinawa sama da 200.

Blinken yace muddin aka kasa samun cigaba wajen samarwa Falasdinawa hanyar rayuwa cikin mutunci da kwanciyar hankali, za’a cigaba da samun tashin hankalin, kuma hakan ba zai taimaki kowa ba.

Wannan matsayi na zuwa ne a daidai lokacin da sakataren ke shirya fara ziyarar aiki a Gabas ta Tsakiya inda ake sa ran zai gana da shugabannin Israila da Falasdinu da kuma shugabannin yankin.

Jaddada wannan matsayi na kafa kasasr Falasdinu da kuma tabbatar da zaman lafiya na daga cikin manufofin Amurka na da kafin zuwan tsohon shugaban kasa Donald Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI