Saudiya - Coronavirus

Mutane dubu 60 ne kawai za su yi aikin Hajjin bana - Saudiya

Masu Ibada a dakin Ka'aba cikin baiwa juna tazara domin dakile yaduwar annobar Korona a birnin Makkah dake Saudiya.
Masu Ibada a dakin Ka'aba cikin baiwa juna tazara domin dakile yaduwar annobar Korona a birnin Makkah dake Saudiya. - AFP

Hukumomin kasar Saudi Arabia sun sanar da cewar maniyata aikin Hajjin bana 60,000 kacal zasu gudanar da ibadar ta wannan shekara sakamakon matakan da ake dauka domin dakile cutar korona.

Talla

Sanarwar tace maniyatan dake tsakanin shekaru 18 zuwa 60 kawai za’a baiwa damar gudanar da Hajjin na bana, kuma dole sai an tabbatar da yanayin lafiyar su domin tabbatar da cewar basu kwanta a asibiti ba a cikin watanni 6 da suka gabata.

Sanarwar ta kuma ce ya zama dole maniyatan su karbi allurar rigakafin cutar korona sau biyu kamar yadda ka’ida ta nuna da kuma gabatar da shaidar haka daga kasashen da suka fito.

Saudiyar ta kuma ce maniyatan zasu aiwatar da okar bada tazara da kuma sanya kyallen dake rufe baki da hanci da kuma Karin matakan kare lafiyar maniyatan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI