Amurka-Rasha

Biden zai gana da Putin a Geneva don gyara alakar Amurka da Rasha

Shugaban Amurka Joe Biden da Vladimir Putin na Rasha.
Shugaban Amurka Joe Biden da Vladimir Putin na Rasha. AP - Alexander Zemlianichenko

Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Rasha Vladimir Putin za su gana a karon farko a Geneva a watan Yuni mai zuwa, abin da ake ganin zai bude sabuwar kofar tattaunawa tsakanin kasashen biyu da ke takun saka da juna.

Talla

Mai Magana da yawun fadar shugaban Amurka Jen Psaki ta sanar da cewar a ranar 16 ga watan gobe shugabannin biyu za su gana a kasar Switzerland.

Wannan shi ne zai zama tafiyar shugaba Biden na farko zuwa kasar waje inda ake saran zai halarci taron kungiyar G7 da NATO da kuma na kungiyar kasashen Turai.

Psaki ta ce shugabannin biyu za su tattauna batutuwa da dama da suka shafi duniya, a kokarin da su ke na daidaita dangantar da ke tsakaninsu.

Dangantaka tsakanin Rasha da Amurka da kuma kasashen yammacin duniya ta yi tsami tun lokacin da Moscow ta mamaye yankin Crimea da ke kasar Ukraine abin da ya sa suka cire kasar daga kungiyar G-8.

Yunkurin tsohon shugaban Amurka Donald Trump na kulla hulda da shugaba Putin ya ci tura saboda yadda kasar ta mayar da shi saniyar ware sakamakon zargin da aka yiwa Rasha na katsalandan lokacin zaben da ya bai wa Trump damar hawa karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI