Majalisar Dinkin Duniya-Belarus

Kwamitin tsaro na MDD zai yi zama na musamman kan Belarus

Shugaban Kasar Belarus Alexander Lukashenko.
Shugaban Kasar Belarus Alexander Lukashenko. Andrei STASEVICH BELTA/AFP/File

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na shirin gudanar da wani zaman sirri yau Laraba don tattauna matakin da Majalisar za ta dauka kan shugaban kasar Belarus Alexandre Lukashenko dangane da karkatar da jirgin Ryanair da ya yi don kame dan jaridar da ke caccakar gwamnatinsa.

Talla

Belarus wadda ke ci gaba da fuskantar takunkuman manyan kasashe, tilasta saukar da jirgin da Lukashenko ya yi a karshen makon jiya ya kara masa karin caccaka daga kasashen Duniya wadanda su ke fuskantar takun saka da kasar tun bayan zaben bara.

Zaman Majalisar na yau zai fayyace matakin da za ta dauka kan Belarus, bayanda tun farko ta bayyana aika-aikar ta Lukashenko a matsayin abin da ba zai karbu ba.

Yanzu haka dai kiraye-kiraye na kara karfi musamman daga kasashen yammaci wajen ganin Lukashenko ya saki matashin dan jaridar wanda ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnatinsa.

Kungiyar Tarayyar Turai na matsayin 'yar gaba gaba da ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da bincike kan Lukashenko bayan matakin tilasta saukar da jirgin na Ryanair, yayinda Rasha ta goyi bayan kasar dangane da matakin.

Acewar Rasha, Belarus ta dauki matakin ne don kare kanta daga kalubalen da dan jaridar ke shirin haifarwa kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI