Amurka-Tusla

Biden na ziyara a Tusla bayan cika shekaru 100 da kisan daruruwan bakar fata

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. MANDEL NGAN AFP

Shugaban Amurka Joe Biden ya fara ziyara a yankin da aka yiwa daruruwan Amurkawa Bakaken fata kisan gilla a Tusla da ke jihar Oklahoma, wanda ke zama daya daga cikin mafi munin rikicin kabilanci a tarihin Amurka shekaru 100 da suka gabata.

Talla

Shugaban Amurka Joe Biden wanda zai yi tattaki zuwa birnin Tusla da ke jihar Oklahoma, zai zama shugaban kasar mai ci na farko da zai taba ziyartar wurin da wasu gungun Amurkawa farar fata suka kashe daruruwan takwarorinsu Bakake a shekarar 1921.

Sanarwar da fadar White House ta fitar na cewa, shugaba Biden zai gana da tsirarun mambobin kungiyar Greenwood, yayin da ake jimamin cika shekaru 100 na tunawa da kisan, inda zai sanar da sabbin matakan yaki da rashin daidaito a kasar.

Sabbin matakan sun hada da tsare-tsaren fadada kwangilolin tarayya da kananan kamfanoni marasa galihu, da zuba jari na biliyoyin daloli ga al'ummomin gundumomi kamar su Greenwood wadanda ke fama da talauci da kuma magance nuna wariya a harkar bada gidaje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI