Coronavirus-Tattalin arziki

Korona ta talauta ma'aikata miliyan 100

Ana fargabar karin miliyoyin ma'aikata za su tsunduma cikin talauci saboda Korona
Ana fargabar karin miliyoyin ma'aikata za su tsunduma cikin talauci saboda Korona REUTERS - LIM HUEY TENG

Annobar Covid-19 da ke ci gaba da lakume rayukan bil’adama bayan kashe wasu fiye da miliyan 3 da rabi, ta jefa karin ma’aikata miliyan 100 cikin talauci kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar.

Talla

Cikin sabon rahoton da ta fitar, kungiyar kwadago ta duniya ILO ta yi gargadin cewa matsalar da annobar Korona ta haifar a fannin kwadago ba za ta kau a nan kusa ba, la’akari da hasashen kwararrun da ya bayyana sai a shekarar 2023 ake sa ran za a samu daidaiton guraben ayyukan yi zuwa matakin da suke a shekarun baya, kafin barkewar annobar Korona.

Rahoton kungiyar kwadagon ya kuma ce, za a samu karanci ko gibin guraben ayyukan yi akalla miliyan 75 a duniya zuwa karshen shekarar da muke ciki ta 2021, idan aka kwatanta da lokacin da annobar Korona ba ta barke ba.

Zalika ko da zuwa karshen shekarar 2022 mai zuwa, sai an fuskanci gibin guraben ayyukan yin miliyan 23 duk dai saboda tasirin wannan annoba ta Korona.

Yawan marasa aikin yi miliyan 205 ake sa ran samu jumilla a dai karshen shekarar ta 2022, adadin da ya zarta na shekarar 2019, lokacin da kididdiga ta nuna yawan marasa aikin a duniya ya kai miliyan 187.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.