G7

G7 na kokarin shawo kan cutuka masu barazana da ake samu daga dabbobi.

Ministocin harkokin wajen kasashen G7 bayan taron su Landan na kasar Birtaniya ranar 4 ga watan Mayu 2021
Ministocin harkokin wajen kasashen G7 bayan taron su Landan na kasar Birtaniya ranar 4 ga watan Mayu 2021 Ben Stansall Pool/AFP

Ministoci daga kasashen Burtaniya da Canada da Faransa da Jamus da Italiya da Japan da kuma Amurka zasu tattauna kan yadda za a shawo kan cutuka masu barazana da ake samu daga dabbobi.

Talla

Kasashen dai na ganin cewa akwai bukatar a dauki matakan gaggawa kan cutuka masu saurin yaduwa da ake samu daga dabbobi, wadanda ke kasancewa barazana gad an adam da kuma muhalli.

Wannan taro dai na zuwa ne yayin da kasashe masu karfin arziki ke fuskantar matsi na kara kaimi don taimakawa matalautan kasashen da suka gaza samarwa kan su alluran rigakafi.

Gwamnatin Burtaniya dai a baya-bayan ta fitar da wani sabon rahoto kan ci gaban da kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G7 tun daga shekarar 2015 kan taimaka wa kasashe masu tasowa samun alluran rigakafi da dakile matsalolin cutuka masu saurin yaduwa.

Shirin Covax

Kamar yadda rahotanni ke cewa, tuni kasashen G7 suka kuduri aniyar tallafawa shirin raba maganin rigakafi Covax.

Ministan lafiya na Burtaniya Matt Hancock ya ce an fitar da sama da rabin biliyan guda na allurar rigakafin AstraZeneca, kuma galibi kasashe masu tasowa ne za su amfana da wannan shiri.

Amma duk da haka ana ci gaba da kiran kasashen da ke da karfin tattalin arziki su kara kaimi, cikin shirin, wanda aka samar tare da hadin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya da Kungiyar Kasuwanci ta Duniya, kan neman a ba da gudummawar kudi na dala biliyan 50.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.